Yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen ziyararsa ta yini daya a birnin Maiduguri a jiya Jumma'a, Ihejirika ya ce, ya zama wajibi ya bayyana godiyarsa, don gane da irin goyon-bayan da matasa masu aikin sa-kai ke nunawa, ta fuskar yaki da masu tada zaune-tsaye. Bugu da kari, ya yabawa Shehun Borno gami da daukacin al'ummar jihar, sakamakon goyon-baya da taimakonsu ga shirin dawoda zaman lafiya jihar da rundunar hadin gwiwa ta JTF ke yi.
Ihejirika ya ce ya ziyarci birnin Maiduguri ne domin ganewa idanunsa irin ci gaba da aka samu, sakamakon kaddamarda bataliyar dakarun soji ta 7 a jihar Borno. Kuma ya tabbatar da cewa hedkwatar rundunonin tsaron kasa na yabawa da ayyukan da suke gudanarwa, kamar yadda ake yabawa ayyukan jami'an rundunar hadin gwiwa ta JTF.
"ina matukar farin-ciki da alfahari da irin yadda wadannan dakaru ke gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada, hakika halayyar da suke nunawa ta burge ni matuka" A kalaman Janar Ihejirika.(Murtala)