in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe wasu masu sace mutane guda 16 a kudancin Najeriya
2013-09-06 10:35:32 cri

Wasu rahotanni da bangaren 'yan sanda a Najeriya ya bayar a ranar Alhamis, ya nuna cewa, an kashe wasu da ake zaton masu sace mutane ne a kalla 16 yayin da aka jikkata wasu 63 a jihar River da ke kudancin Najeriya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Joseph Mbu, ya bayyana a taron manema labarai a garin Fatakwal, babban birnin jihar cewa, an tusa keyar mutane 29 da ake zargi zuwa kotu.

Mbu ya ce, rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahoton koken sace mutane guda 16, inda ya ce, an samu nasarar kubutar da mutane 19 cikin aikace-aikace sace mutane 16, yayin da masu aikata wannan danyen aikin suka kashe mutane 2 da suka sacen.

Mbu ya kara da cewa, nan gaba kadan, za a kawo karshen lamarin a jihar, kana ya yi kira ga jama'a da su rika sanar da 'yan sanda muhimman bayanai da za su kai ga damke wadannan bata gari. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China