Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a ranar Alhamis cewa, a kalla mutane 15 ne suka halaka a wasu hare-hare guda biyu da ake zaton kungiyar nan ta Boko Haram ce ta kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wani jami'i a jihar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce, a ranar Laraba da maraice ne maharan suka yiwa garin Gajiram da ke karamar hukumar Nganzi dake jihar ta Borno tsinke, inda suka halaka a kalla mutane 10.
Jami'in ya ce, galibin mazauna yankin sun famtsama cikin daji ne don neman tsira da rayukansu, maharan sun kuma kai hari kan sakatariyar karamar hukumar da kuma ofishin 'yan sandan yankin.
Wani mazaunin garin da shi ma ya ranta cikin na kare mai suna Babagoni Bashir, ya ce, baya ga maharan da suka abkawa garin Gajiram, wasu gungun maharan sun sake abkawa garin Bulablin Ngaura da ke karamar hukumar Konduga a ranar Alhamis da safe, inda suka kashe mutane 5.
Sai dai har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, hukumomin soja ba su yi wani karin bayani game da hare-haren guda biyu ba. (Ibrahim)