in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mahara sun hallaka mutane biyar a jihar Plateau ta Najeriya
2013-09-03 10:51:43 cri

A Najeriya, wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun hallaka mutane biyar, bayan da suka budewa iyalan wani gida dake kauyen Kunte, a karamar hukumar Jos ta Kudu wuta.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Plateau Felicia Anselm, harin na ranar Lahadi wani salo ne na aikin ta'addanci, wanda ba shi da alaka da fadan addini ko na kabilanci.

Anselm ta kara da cewa, farmakin 'yan bindigar ya ritsa da rayukan magidanci daya, da matarsa, da kuma yaransu uku. Ta ce, tuni jami'an rundunar suka bazama domin gano maboyar wadanda suka aikata wannan danyen aiki, da nufin gurfanar da su gaban kuliya.

Daga shekarar 2001 zuwa 'yan shekarun baya bayan nan, jihar ta Plateau dake yankin tsakiyar Najeriya ta sha fama da rigingimu, masu alaka da banbancin addini da na kabilanci, lamarin da ya sabbaba rasuwar dubban rayukan al'umma, tare da janyo asarar dukiyoyi masu tarin yawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China