Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana kudurinta na aiki tare da masu ruwa da tsaki a harkar man ja, ta yadda za su noma tare da bunkasa bangaren man ja bisa tsarin farfado da masana'antu na gwamnatin tarayyar kasar.
Mnistan masana'antu, cinikayya da harkokin zuba jari na Najeriya Mr. Olusegun Aganga ne ya bayyana hakan, yayin ganawa da dandalin masu harkar noman man ja na Najeriya, kungiyar masu samar da man ja ta Najeriya da kungiyar masu noman danyen kaya da sarrafa man da ake amfani da shi ta Najeriya a Abuja.
Aganga ya ce, babu wata kasa a duniya da ta bunkasa ta hanyar dogaro diyani kan samarwa da kuma fitar da albarkatun ta kadai, ba tare da ta inganta bangaren masana'antunta ba. Ya ce, Allah ya albarkaci Najeriya da tarin albarkatun jama'a da na karkashin kasa, ta yadda za ta iya bunkasa kanta cikin 'dan kankanin lokaci bisa la'akari da gyare-gyaren da gwamnatin shugaba Jonathan ke aiwatarwa.
Ministan ya ce, tuni ma gwamatin Najeriya ta fara aiwatar da shirin farfado da masana'antun kasar, kamar bangaren aikin gona, kuma gwamnatin za ta hada kai da masu ruwa da tsaki a bangaren harkar man ja, ta yadda za a fito da wasu manufofin da za su kai ga bunkasa wannan sashi.
A jawabinsa yayin ganawar, sakataren dandalin Mr. Fatai Afolabi, ya bukaci ma'aikatar masana'antu, cinikayya da zuba jari ta Najeriya, da ta taimaka yadda za a zamanantar da wannan sashi, yana mai cewa, masu ruwa da tsaki a wannan harkar a shirye suke su shiga a dama da su a cikin shirin gwamnati na farfado da masana'antu, ta yadda za a ciyar da bangaren gaba. (Ibrahim)