in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Rasha
2013-09-05 19:25:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Saint Petersburg, a ranar Alhamis 5 ga wata.

A lokacin ganawarsu, shugaba Xi Jinping yayi bayani game da ziyarsa da ya kai kasar a watan Maris na bana wadda yace an samu nasara sosai wanda a sakamakon hakan ne bangarorin 2 suka yi namijin kokari don aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a wancan lokacin, ta yadda ayyukan hadin gwiwa 50 wadanda suka shafi fannoni 16 suka samu ci gaba tare da samar da hakikanin sakamako.

A halin yanzu, in ji Shugaba Xi, da shi da takwaransa na Rasha suna dora muhimmanci sosai kan hadin kan bangarorin 2,don haka suna fatan kara azama ga hadin gwiwarsu a fagen manyan ayyukan da suka shafi tsare-tsare masu muhimmanci, kamar makamashi, zirga-zirgar jiragen sama, da dai sauransu, da karfafa hadin kai a fannin soja, don tinkarar barazanar da ka iya fuskanta a nan gaba.

A nasa bangaren, shugaba Vladimir Putin ya ce kasashen Rasha da Sin na kokarin raya huldar dake tsakaninsu, inda su shugabannin 2 su kan tuntubi juna, kana hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen 2 na samun ci gaba. Wannan yanayin, a cewar Mista Putin, ya gamsar da shi inda ya ce, za a kara daddale yarjeniyoyi da yawa a wannan rana, wadanda za su karfafa tushen dangantakar hadin gwiwar kasashen 2 a nan gaba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China