in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya isa St. Petersburg don halartar taron koli na G20
2013-09-05 10:32:24 cri

A ranar Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin St. Petersburg na kasar Rasha don halartar taron kolin kungiyar kasashen G20 da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis da Jumma'a.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda kasarsa ke karbar shugabancin karba-karba na taro na wannan shekara, ya bayyana cewa, manyan manufofin taron kolin su ne taimakawa wajen karfafa tatalin arziki duniya, dorewa da kuma daidaiton bunkasa.

Kafin ya tashi daga kasar Sin don halartar taron kolin, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan taron kolin na St. Petersburg da ya mayar da hankali kan bunkasa da samar da aikin yi don kara inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar G20, karfafa tsarinsu na tattalin arzikin kasa, kana su hada gwiwa don kyautata makomar tattalin arzikin duniya.

Ana sa ran yayin taron, shugaba Xi ya gana da wasu shugabannin kasashe, ciki har da shugaba Putin na Rasha, Barack Obama na Amurka da kuma shugabannin kasashen Turai da na BRICS.

A yau ne shugaba Xi Jinping ya tashi zuwa Turkmenistan, zangonsa na farko a rangadin da yake a kasashen ketare, inda ake sa ran zai ziyarci kasashen Kazakhstan, Uzbekistan da Kyrgyzstan, bugu da kari zai halarci taron kolin hadin gwiwa na Shanghai da za a yi a Kyrgyzstan. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China