in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugabar kasar Argentine
2013-09-05 16:17:12 cri
Yau Alhamis 5 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kasar Argentine Cristina Fernandez a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.

Yayin ganawarsu, shugaba Xi jinping ya nuna cewa, kullum kasar Sin tana mai da hankali sosai kan raya dadaddiyar dangantakar zumuncin da ke tsakaninta da Argentine, kuma tana son ci gaba da inganta hadin gwiwar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. Sin tana goyon bayan kasar Argentine wajen ba da gudumawa cikin harkokin kasa da kasa, kuma a matsayinsu na kasashe masu samun saurin ci gaban tattalin arziki, ya kamata su yi kokari tare domin karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka, tare kuma da kiyaye moriyar kasashe masu samun saurin ci gaba da kuma kasashe masu tasowa.

A nata jawabi, shugaba Cristina Fernandez ta bayyana cewa, kasar Argentine tana son kara fitar da hajojin kasar zuwa kasar Sin kuma tana maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin a kasarta don ba da taimako wajen samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, kamar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa da kuma layukan doga da dai sauransu, ta yadda kasar Sin za ta iya shiga kasuwannin Latin Amurka karkashin taimakon da kasar Argentinu ke samar mata. Bugu da kari, kasar Argentine tana son karfafa cudanya tsakaninta da kasar Sin kan harkokin kasa da kasa da kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China