Da yake tabbatar da aukuwar hakan, kakakin rundunar dake jihar ta Sakkwato, Yahaya Musa ya ce, an kai simame maboyar 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram dake unguwar Gidan-Igwai a ranar Asabar 10 ga wata, bayan samun wasu bayanan sirri. Musa ya ce dukkanin matakan da ake dauka na da nasaba da burin rundunar, na tabbatar da doka da oda, tare da kare rayukan al'umma daga barazanar ayyukan 'yan ta da kayar baya.
Daga nan sai ya tabbatar da aniyar jami'an tsaro, ta tabbatar da gurfanar da dukkanin wadanda aka kama sakamakon wannan farmaki gaban kuliya, kamar yadda doka ta tanada.
Wannan dai mataki na zuwa ne dai dai lokacin da ake ci gaba da fargaba, don gane da yiwuwar cimma nasarar shirin gwamnatin tarayyar Najeriyar na yi wa 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram afuwa, wanda aka fara cikin watan Afrilun da ya gabata. (Saminu Alhassan)