A ran 5 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sham ya bayyana cewa, kasar ta yarda da kungiyar Tarayyar kasashen Larabawa AL da ta tura tawagar sa ido zuwa kasar, kuma za su kulla yarjejeniya ba tare da bata lokaci ba. Amma kungiyar AL ta sanar da cewa, ba za ta fasa saka takunkumi ga kasar Sham ba. Game da haka, a gun taron manema labaru da aka shirya a birnin Beijing, Hong Lei ya bayyana cewa, a ganin kasar Sin, ya kamata kasashen duniya su kiyaye moriyar Sham da kiyaye zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya, da kafa yanayi mai kyau wajen warware batun Sham, wannan shi ya dace da babbar moriyar jama'ar kasashen Gabas ta tsakiya da na kasashen duniya.(Abubakar)