in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya tashi zuwa birnin St.Petersburg don halartar taron G20
2013-09-04 20:12:49 cri
Bayan kammala ziyararsa a kasar Turkmenistan, a ranar Laraba 4 ga wata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Mary zuwa St.Petersburg na kasar Rasha, domin halartar taron koli karo na 8 na shugabannin G20 da za a yi a ranar 5 da 6 ga wata.

Turkmenistan ta kasance kasa ta farko da shugaba Xi ya kai ziyara a tsakiyar Asiya a wannan karo.

A jiya 3 ga wata, bayan isar sa birnin Ashgabat, shugaba Xi ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Turkmenistan, Gurbanguly Berdimuhamedow, inda shugabannin biyu suka darajanta ci gaban dangantaka tsakanin kasashen biyu, da tsara fasalin hadin gwiwa tsakaninsu a nan gaba, kuma sun yanke shawarar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu.

Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun rattaba hannu kan hadaddiyar sanarwa dangane da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Turkmenistan, tare da halartar bikin daddale yarjeniyoyin hadin gwiwa a fannonin diplomasiyya, tattalin arziki, cinikayya, makamashi da sauransu.

Kafofin yada labaru na ganin cewa, ziyarar shugaba Xi a wannan karo ta karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, tare da bude wani sabon babi na bunkasa dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China