A lokacin wannan ziyara shugaba Xi zai rattaba hannu kan muhimmin yarjejeniyar siyasa da Shugaba Berdimuhamedow, tare da halartar bikin daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kamfanoni na kasashen biyu. Daga bisani kuma shugabannin biyu za su gana da manema labarai.
Kasar Sin ta kulla huldar diplomasiyya da Turkmenistan a shekarar 1992, daga bisani sun bunkasa dangantaka tsakaninsu lami lafiya. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, shugabannin kasashen biyu sun yi mu'amala tsakaninsu sosai, tare da karfafa hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, cinikayya, makamashi da sauransu tsakanin kasashen biyu, tare da samun babbar nasara. (fatima)