A lokacin ziyarar tasa, shugaba Xi Jinping zai yi shawarwari da takwaransa na Turkmenistan Gurbanguly Berdimuhamedow. Ana kuma fatan cewa shugabannin biyu, za su daddale, su kuma gabatar da takarda mai kunshe da irin nasarorin da suka cimma bayan tattaunawar tasu, kana hukumomin da abin ya shafa na kasashen biyu, da masana'antun kasashen biyu, su ma za su daddale jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a tsakaninsu.
Turkmenistan zango ne na farko a ziyarar da shugaba Xi Jinping ke yi a wannan karo. Inda baya wannan kasa, ake sa ran zai ziyarci kasashen Kazakhstan, da Uzbekistan, da kuma Kyrgyzstan. Kana zai halarci taron koli na kungiyar G20 da za a gudanar daga ranar 5 zuwa 6 ga wata a birnin St. Petersburg na kasar Rasha da kuma taron koli karo na 13, na kungiyar hadin kai ta Shanghai, wadda za a gabatar a ranar 13 ga wata a birnin Bishkek na kasar Kyrgyzstan. (Bilkisu)