A ranar Talata, jakadan MDD kan batun Syria Lakhdar Brahimi ya yaba ganawa tsakanin jami'an kasashen Amurka da Rasha, wadda aka shirya yi tun a baya, domin a yi shirye shiryen gudanar da taron kasa da kasa da aka jinkirta na tsawon lokaci, dangane da kasar Syria wacce take fama da rikici.
Cikin wata sanarwa daga ofishin mai magana da yawun MDD, an ce, wakilin hadin gwiwa na musamman kan kasar Syria na MDD, Lakhdar Brahimi yana maraba da wannan tattaunawa tsakanin kasashen biyu kan rikicin kasar Syria wadda za'a yi tsakanin jami'an kasashen Rasha da Amurka a Hague nan ba da dadewa ba.
Sanarwar ta kara da cewa, Mr. Brahimi ba zai kasance cikin ganawar ba.
A ranar Litinin, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Rasha, Gennady Gatilov, ya baiyana cewa, zai gana da wata tawaga daga Amurka a cikin mako mai zuwa a Hague, domin yin shawarwari kan shiryen-shiryen gudanar da taron zaman lafiya don a kawo karshen yakin basasa a kasar Syria.
A kuma fadin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka, wannan ganawa da za su yi ta biyo bayan wata yarjejeniya ce da aka cimma yayin tattaunawa da aka yi a Washington ranar 9 ga watan Agusta, tsakanin ministotin harkokin waje da na tsaro na kasashen biyu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kila a gudanar da wani taron nan ba da dadewa ba, ko da yake ba'a tsai da shawarar ranar da za'a yi ba, domin a kara yin shirye-shiryen taron na Geneva taki na biyu. (Lami)