Sakamakon karshe na zaben shugaban kasar ta Mali zagaye na biyu na ranar 11 ga watan Agusta wanda ya hada takara tsakanin Ibrahim Boubacar Keita da Soumaila Cisse, za'a fitar da shi a wannan ranar Talata da safe, cewar shugaban kotun kolin kasar Mali, mista Amadi Tamba Camara a cikin wata sanarwar da aka fitar ranar Litinin.
A cewar alkaluman sakamakon wucin gadi na ranar Alhamis da ta gabata da ministan hukumomin kasar Mali janar Moussa Sinko Coulibaly ya bayar, 'dan takarar jim'iyyar RPM, Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani da IBK ya lashe zaben shugaban kasa zagaya na biyu na ranar Lahadin da ta gabata da kashi 77,61 cikin 100 a gaban abokin takararsa Soumaila Cisse na jam'iyyar URD wanda ya samu kashi 22,39 cikin 100. Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar Mali ya tanada, za'a rantsar da sabon shugaban kasa makonni biyu bayan samun sakamakon karshe. (Maman Ada)