Shugaban kasar Sin ya tashi daga nan birnin Beijing don kai ziyara kasashe hudu na tsakiyar Asiya, da halartar tarukan koli biyu
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tashi daga nan birnin Beijing a safiyar yau Talata 3 ga wata, don kai ziyarar aiki kasar Turkmenistan, kana zai halarci taron koli na kungiyar G20 da za a shirya a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, daga baya kuma zai kai ziyarar aiki kasashen Kazakhstan, Uzbekistan, da kuma Kyrgyzstan, a Kyrgyzstan shugaba Xi zai halarci taron koli karo na 13 na kungiyar hadin kai ta Shanghai da za a shirya a Bishkek.
Wannan ne karo na 3 da Xi Jinping ya kai ziyara kasashen ketare tun bayan da ya zama shugaban kasar Sin. (Bilkisu)