in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika ya kyautata zaman rayuwar jama'ar kasashen na Afrika
2013-03-25 15:38:01 cri






Shekarun baya bayan nan, bisa karuwar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, an tafiyar da manyan ayyukan hadin gwiwa daban daban a kasashen Afrika, wadanda suka gudana karkashin jagorancin gwamnatocin bangarorin biyu, ta yadda aka kyautata zaman rayuwar jama'ar kasashen, ciki hadda gina hanyoyin mota, inganta tsarin sadarwa, da aikin jinya, da kuma ba da ilmi.

Wadannan manyan ayyuka ma sun inganta kayayyakin more rayuwa na kasashen Afrika, tare kuma da aza harsashi mai kyau, ga bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar su. Gaskiya ne hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika dake karuwa, ya canja hanyar zaman rayuwar jama'arsu sannu a hankali.

A birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya dake gabashin Afrika, ana iya ganin wasu irin babura masu daukar fasinja a ko ina, wadanda mutanen wurin suke kira "bodaboda". Wasu daga cikinsu masu alamar "Sanlg" kirar kasar Sin, sun kai kaso mai yawa na baburan. Irin wadannan babura na da inganci, kuma farashinsu na iya samun karbuwa ga jama'ar wurin, hakan ya sa su bazuwa a duk fadin kasar.

Karbuwa da baburan masu kirar kasar Sin ke samu a kasuwar Tanzaniya, ta sanya masu cinikinsu samun kudin shiga da yawa, sakamakon shigowar su kasar, amma abin da ya fi jawo hankali, da kuma bayar da mamaki shi ne, sana'ar babura masu zirga-zirga na taka muhimmiyar rawa ga tsaron al'ummar wurin.

Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Tanzaniya ta bayar, an nuna cewa, yawan mutanen da suka rasa aikin yi a kasar ya kai kashi 10.7 cikin kashi 100, matasa da yawa sun dade suna cikin yanayin rashin aikin yi, sakamakon karancin ilmi da horo. Matsakaicin kudin da suke kashewa wajen zaman rayuwa a ko wace rana ya kai sule 500, wato kimanin kudin Amurka cent 30. Bisa ma'aunin da MDD take bi, mutanen da yawan kudin zaman rayuwarsu kan kowace rana ya gaza dalar Amurka 1.25, na cikin masu fama da talauci.

Saboda rashin samun kudin shiga, wasu suna aikata laifuffuka na sata da fashi. Amma, bayan bullowar wadannan babura masu daukar fasinja, an dauki wasu daga matasan da ba su da aikin yi don zama matukan baburan, aikin da ke iya taimaka musu wajen ci gaba da zaman rayuwarsu, ta yadda ba za su aikata laifuffuka ba.

Wani direban babur mai suna Ramadhani Juma ya gayawa wakilimmu cewa, aikin tukin ya kawo masa kudin shiga da yawa, yawan kudin da yake samu a ko wace rana ya kai sule dubu biyar zuwa dubu 20.

Masu aikin tukin a kasar ta Tanzaniya suna da yawa, hakan ya sa aka samu ci gaba wajen sayar da tufafi, da takalma, da huluna, da wayar salula da sauran kayayyaki a kasar. Ciki wannan adadi kuwa, kusan ko wane direba yana da salula guda, domin yin mu'amala tare da fasinja. Kashe kudi don saye da amfani da salula, ya kasance daya daga dalilin dake inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

A Nijeriya kuwa, wadda ke yammacin Afrika, janaretoci masu kirar kasar Sin na amfanar jama'arta, a fannonin zaman rayuwa da ayyukansu. Rashin samun isasshiyar wutar lantarki, babbar matsala ce a kasar, lamarin da ya hana bunkasuwar tattalin arziki, tare da kawo mummunan tasiri ga zaman rayuwar jama'a. 'Yan kasuwa na bukatar wutar lantarki don ba da tabbaci wajen gudanar da harkokin cinikayya, jama'a ma na bukatar wutar lantarki don tabbatar da zaman rayuwarsu na yau da kullum.

Saboda haka, dole ne su sayi janaretoci. Janaretoci iri daban daban masu kirar kasar Sin, suna samun karbuwa sosai a kasar, sakamakon inganci, da farashin mai rahusa. Wani mazaunin birnin Lagos dake kudancin kasar ya gaya mana cewa, shekara daya ke nan da ya sayi wani janareta mai kirar kasar Sin, amma har yanzu bai yi samu wata matsala ba, ga shi kuma yana biya masa bukatu kusan a dukkanin kayayyakin wutar lantarki. Abokansa da yawa su ma sun sayi janaretocin da aka kera a kasar ta Sin. A kasuwar Jakandi dake birnin Ikko, rumfuna da dama na cin gajiyar janaretoci kirar kasar Sin. Wani mai sayar da kifi ya gaya ma wakilinmu cewa, ba ya damuwa ga batun lalacewar kifinsa ba, saboda daukewar wutar lantarki, tun da dai ya sayi janareta na kashin kansa.

Rahotanni sun nuna cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika na kara taka muhimmiyar rawa kan zaman rayuwar jama'ar kasashen Afrika, suna kuma taimakon su wajen warware matsaloli, ko kawo musu alheri. Ko da yake irin wadannan sauye-sauye ba su cika jawo hankali sosai ba idan an kwatanta su da wasu manyan ayyukan gwamnatoci, amma duk da haka suna da ma'ana sosai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China