in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun kasar Sin sun yi sharhi game da ziyarar shugaban kasar ta farko a kasashen waje
2013-03-21 18:29:26 cri






A ranar 22 ga wata da safe, shugaban kasar Sin zai bar birnin Beijing don kai ziyara a kasashen Rasha, Tanzaniya, Afrika ta kudu, da Kongo(Brazzaville), kuma zai halarci shawarwari karo na 5, na shugabannin kungiyar kasashen BRICS da za a yi a birnin Durban da ke kasar Afrika ta kudu. Haka kuma, Ziyarar kwanaki 9 za ta zama ziyara ta farko ta shugaban Xi tun bayan da ya hau kujerar shugaban kasar Sin. Yayin da kwararrun kasar Sin ke zantawa da wakilinmu game da batun, sun bayyana cewa, wannan labari ya nuna manufar diplomasiyya ta kasar Sin, da muhimmiyar rawar da kasashe maso tasowa da kasashen BRICS za su taka a ci gaban duniya.

Ziyarar farko da shugaban kasar Sin zai kai a kasashen waje ta jawo hankalin kasashen duniya, inda ta nuna alkiblar manufar diplomasiyya ta sabuwar gwamnatin kasar Sin. An lura cewa, ziyarar farko da shugaban Xi zai kai ta kunshi nahiyar Asiya, Turai, da Afrika, shugaban cibiyar nazarin al'amuran kasa da kasa ta Sin Qu Xing, ya bayyana cewa, hakan ya haskaka manufar diplomasiyyar kasar Sin, ya ce, "Dangantakar da ke tsakanin Sin da manyan kasashen duniya tana da ma'ana ta musammna gare ta, sa'an kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashe makwaftanta ita ma tana da muhimmanci gaske, baya ga wannan kuma, dangantakar dake tsakaninta da kasashe masu tasowa ta zama wani tushe cikin harkokin diplomasiyyar kasar, a karshe dai, dangantakar bangarorin daban daban, ta zama wani muhimmin dandali ga kasar , haka kuma ziyarar farko da shugaba Xi zai kai a kasashen waje. La'akari da cewa, Rasha wata kasa ce da ke cikin kwamitin sulhu na M.D.D., sannan kuma wata babbar kasa a fadin duniya, kuma kasa mafi girma da ke makwabtaka da kasar Sin, dole ne Sin ta mai da hankali sosai game da dangantakar da ke tsakaninsu. Ban da wannan kuma, kasashen Afrika wakilai ne na kasashe masu tasowa ne, kazalika kuma, kungiyar kasashen BRICS, ta zama wani tsarin diplomasiyya na bangarori daban daba.

A cikin 'yan shekarun nan da muke ciki, shugabannin kasashen Sin da na Rasha, sun mayar da kasashen juna, na farko da za su ziyarta bayan da suka hau karagar mulki, kwararrun sun bayyana cewa, hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha na dada samun bunkasuwa. Kwararre mai nazarin batun Rasha a cibiyar nazarin harkokin kimiyya da zamantakewar al'umma ta Sin Jiang Yi, ya nuna cewa, kasashen Sin da Rasha za su mai da hankali a kan inganta hadin gwiwa a tsakaninsu, ya ce, "Yayin da ake hadin gwiwa game da makamashi da sauran manyan ayyuka a tsakaninsu, a cikin 'yan shekarun nan da ake ciki, kasashen Sin da Rasha sun tattauna inganta hadin gwiwa ta fannin makamashi da manyan ayyuka a tsakaninsu, don sa kaimi ga saka jari, da yin hadin gwiwa, matakin da ya nuna alkiblar inganta hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu a nan gaba. Wato ba ma kawai za a mai da hankali game da yawan cinikayya a tsakaninsu ba, a'a har ma da batun mai da hankali ga inganta hadin gwiwar bangarorin biyu."

Game da ziyarar Shuagaba Xi a kasashen Afrika 3, tsohon manzon musamman na gwamnatin Sin game da harkokin kasashen Afrika Liu Guijin ya bayyana cewa, ziyarar da Shugaban zai kai na da ma'anar musamman, sabo da za a tattauna batun mai da hankali game da zaman lafiya da karko a kasashen Afrika, da kara saka jari game da masana'antun kirkire-kirkire a kasashen Afrika, da inganta raya hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Game da wannan, kwararriyya a tsangayar nazarin harkokin yammacin Asiya da nahiyar Afrika, na cibiyar nazarin kimiyya da zamantakewar al'umma ta kasar Sin He Wenping, ta bayyana cewa, dalilin da ya sa shugaban kasar Sin ya zabi kasashen Afrika cikin zangon ziyarar farko da zai kai, shi ne,"Na farko dai, hakan ya nuna cewa, Sin tana dora muhimmanci sosai kan kasashen na Afrika, kasancewar Afrika nahiyar da ke da kasashe masu tasowa mafi yawa, ban da wannan kuma, manufar da kasar Sin take bi game da kasashen Afrika ba za ta canja ba, matakin da ya nuna cewa, sabbain shugabannin kasar Sin za su ci gaba da dora muhimmanci sosai game da dangantakar da ke tsakanin kasar ta Sin da kasashen Afrika.

Haka kuma, an ce, daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga wata, shugabannin kasashen kungiyar BRICS, za su hallara a birnin Durban dake kasar Afrika ta kudu, don yin musayar ra'ayi game da karfafa dangantakar abokantaka da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China