in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala jefa kuri'a zagaye na biyu na babban zaben kasar Mali
2013-08-12 15:21:31 cri

An kammala jefa kuri'a a zagaye na biyu na babban zaben kasar Mali da misalin karfe 6 na yammacin ranar Lahadi 11 ga wata, a wannan ranar kuma ba'a samu tashin hankali da sauran al'ammurra na ba zata ba.

Bisa labarin da kungiyar masu sanya ido kan zaben da suka fito daga kasar Mali ta bayar, an ce, an gudanar da jefa kuri'a zagaye na biyu na babban zaben ne cikin lumana a jiya Lahadi. Tashoshin jefa kuri'a da yawansu ya kai kashi 77.5 cikin dari na duk fadin kasar sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Haka kuma kungiyar masu sanya ido kan zaben ta nuna cewa, yawan masu zabe da suka jefa kuri'unsu kan zaben na zagaye na biyu ya ragu kadan in an kwatanta da na zagayen farko, wanda yawansu ya kai kashi 48.98 cikin kashi dari.

Bayan da aka gama wannan jefa kuri'a, wasu tashoshin Intanat da gidajen rediyo da sauran kafofin watsa labaru na kasar Mali sun sanar da sakamakon kidayar yawan kuri'u na wasu tashoshin jefa kuri'a, inda aka nuna cewa, yawan kuri'un da Ibrahim Boubakar Keita ya samu ya fi na Soumaila Cisse bisa rinjaye.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China