in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga 'yan takarar babban zaben kasar Mali da su karbi sakamakon zaben da zuciya daya
2013-08-11 17:07:42 cri
Har yanzu dai muna kasar ta Mali, inda shugaban hukumar gudanar da zaben kasa, Mamadou Diamoutani, ke kira ga 'yan takara biyu da suka rage a zagayen babban zaben kasar na biyu, da su karbi sakamakon zaben da za a kada a lahadin nan da zuciya guda.

A sakonsa na ranar Jumma'a, 'yan sa'o'i kadan kafin kammalar wa'adin yakin neman zaben, Diamoutani ya yabawa dukkanin 'yan takarar da suka shiga zagayen farko, bisa sha'awar da suka nuna ga zaben, da ma amincewar da suka yi ga sakamakon zaben na farko. Har ila yau jagoran hukumar zaben ta CENI, ya yabawa 'yan tagara Biyu da suka rage a zagayen zaben na Biyu, don gane da kyakkyawan misali da suka nuna, na gudanar da yakin neman zabe lami lafiya.

Ya ce al'ummar Mali da ma daukacin kasashen duniya na da kyakkyawan fatan 'yan takarar Biyu za su martaba sakamakon zaben da zarar an bayyana shi. Bugu da kari Diamoutani ya ce hukumarsa za ta tabbatar da daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin ganin an aiwatar da sahihin zaben a wannan zagaye na Biyu. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China