in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kara fitar da bayani game da hadin gwiwa a tsakaninta da Afrika ta fuskar tattalin arziki da cinikayya
2013-08-29 17:10:31 cri

A yau Alhamis 29 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labaru game da bayanin da ta fitar a kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, inda aka nuna yadda aka samu bunkasuwar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya bayan shekarar 2010.

Bisa kididdigar da aka yi an nuna cewa, kasar Sin ta kasance aminiyar kasashen Afrika ta fuskar cinikayya da ta fi girma a duniya a cikin shekaru 4 da suka wuce a jere, kuma ita ce babbar abokiyarsu ta hadin kai wajen samun bunkasuwa, da sabuwar kasa dake zuba jari a kasashen. A nasu bangaren ma, kasashen Afrika ya zama muhimmin yanki dake shigar da kayayyaki daga kasar Sin, kuma babbar kasuwarta ta biyu wajen yin kwangilar gine-gine, da kuma babban yanki na 4 da Sin ke zuba jari a kai.

A yayin taron manema labaran mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin mista Li Jinzao ya bayyana cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Afrika na samun saurin bunkasuwa, nan gaba kuma za su ci gaba da kokari tare don kafa wata kungiyar gamayyar samun bunkasuwa tsakaninsu. Mr Li wanda ya lura cewa, an samu tabarbarewar tattalin arzikin duniya a shekarar 2012, ya ce duk da haka jimilar kudi da aka samu wajen cinikayya a tsakanin Sin da Afrika ta wuce dalar Amurka biliyan 198, wato karuwarta ta kai kashi 19 cikin 100 yana ganin cewa, an samu wannan ci gaban ne sakamakon yanayin da bangarorin biyu ke ciki.

"Da farko, kasashen Afrika na bukatar kayayyakin kasar Sin sosai domin biyan bukatunsu na samun cigaba. Na biyu, yanzu kasashen Afrika na cikin yanayi mai karko ta fannin siyasa. A nasa bangaren kuma, kasar Sin ta samu karfin zuba jari bayan shekaru goma da yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Bayan haka kuma, Sin da kasashen Afrika na bukatar juna ta fuskar tattalin arziki."

A yayin taron ministoci karo na 5 game da dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika, wanda aka shirya a bara, gwamnatin kasar Sin ta sanar da sabbin matakan da za ta dauka a fannoni guda 5 da nufin inganta hakikanin hadin kai a tsakanin bangarorin biyu, ciki kuwa har da karfafa hadin gwiwa kan zuba jari da tattara kudi, ba da tallafi don samun bunkasuwa, da kuma nuna goyon baya ga yunkurin dunkulewar kasashen Afrika, dukkan su na shafar harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Cikin shekara daya da ta wuce, ta yaya aka gudanar da matakan? Shugabar sashen kula da harkokin kasashen yammacin Asiya da Afrika na ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, madam Zhong Manying ta amsa da cewa,

"A fannin zuba jari da tattara kudi, mun yi alkawarin samar wa Afrika kudi na dalar Amurka biliyan 20. Yanzu mun riga mun daddale yarjejeniyoyi da wasu kasashe game da ba da rancen kudi mai gatanci da na cinikayya, domin taimaka masu wajen raya kayayyakin more rayuwa, masana'antu, sufuri, sadarwa da sauransu. A fannin ayyukan ba da tallafi kuwa, ana gudanar da su lami lafiya, ciki har da samar da sauki ga cinikayya da zuba jari, aikin jinya da kiwon lafiya, ba da ilmi, al'adu, horar da kwararru, da kuma kiyaye muhalli."

A gun taron manema labaru, mataimakin ministan harkokin cinikayya Li Jinzao ya ambaci wannan kalma sau da dama "kungiyar gamayyar samun bunkasuwa tsakanin Sin da Afrika". Inda ya bayyana cewa, a farkon shekarar da muke ciki, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya zabi wasu kasashen Afrika a matsayin zangonsa na farko wajen yin ziyara bayan ya hau kujerarsa, wannan ya nuna babbar niyyarsa ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu. Li ya ce,

"Afrika muhimmiyar kasuwa ce ta kasar Sin a kasashen ketare, kana kuma yankin zuba jari, da na neman makamashi. Kazalika bunkasuwar Afrika na bukatar samun fasahohi, kudi, kwararru daga kasar Sin, hakan ana iya cewa suna dogaro sosai wajen samun bunkasuwa. Ko kasar Sin, ko kuma kasashen Afrika dukkansu sun fahimci cewa, ba su iya rabuwa da junan su, kuma suna bukatar gudanar da hakikanin hadin kai bisa tushen zaman daidaituwa da samun moriyar juna."

Bayan haka kuma, Li ya bayyana cewa, a nan gaba ban da kyautata hanyar hada kai, kasar Sin da kasashen Afrika za su kara habaka fannonin hadin gwiwa,domin kara biyan bukatun jama'a. Hakazalika, ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara kokarinta don samar wa masana'antu wani muhalli mai kyau wajen hadin gwiwa, da nufin kwantar musu da hankali lokacin da suke gudanar da harkokin cinikayya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China