in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar da ke tsakanin Sin da Afrika za ta samu makoma mai haske
2013-02-18 18:01:13 cri
A ranar 17 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Afrika, don inganta hadin gwiwa game da manyan batutuwan da suka shafi shimfida zaman lafiya, da harkokin tsaro a kasashen na Afrika, da karfafa dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zuwa wani sabon matsayi.

Wannan shi ne karo na farko da Xi Jinping, ya gana da shugabar kwamitin kungiyar AU, bayan da ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Duba da cewa, nan ba da dadewa ba, za a samu sauyin shugabannin kasar Sin, ina aka kwana game da dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika? Shugaban cibiyar nazarin batun kasa da kasa Qu Xing ya bayyana cewa, babban tushen da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ba zai sauya ba, sabo da a cikin wani dogon lokaci mai zuwa, kasar Sin da kasashen Afrika za su ci gaba da zama kasashe masu tasowa.

Da ma daga shugabannin kasashen Afrika da suka kulla kyakkyawar dangantaka da kasar Sin yayin da suke fafutukar neman 'yancin kai, sun bar karagar mulki, wannan ya kawo wani sauyi game da dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, Qu Xing ya bayyana cewa, "Yayin da kasashen Afrika suke fafutukar neman 'yancin kai, tsoffin shugabanninsu sun kulla kyakkyawar dangantaka da kasar Sin, kuma sun san kasar Sin sosai, amma yanzu dukkan wadannan tsoffin shugabannin sun bar karagar mulki, kuma sabbin shugabannin da suke mulki yanzu, sun samu ilmi a kasashen yammacin duniya, sabo da haka, tunaninsu da kuma fahimtarsu game da kasar Sin ya bambanta matuka, ban da wannan kuma, huldar tattalin arziki da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta canja daga gudummawar da Sin ta bayar kawai zuwa samun moriya da cimma nasara tare, sabo da haka, wasu daga jama'ar Afrika ba su saba da hakan sosai ba.

Idan kuwa aka tabo maganar rashin daidaito game da cinikayyar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, Qu Xing ya bayyana cewa yanzu, game da halin da ke ciki tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kasashen Afrika sun samu rarar ciniki, yayin da suke yin cinikayya da kasar Sin, sabo da haka, kamata ya yi a lura da kiki-kakar ciniki da ke tsakaninsu, ya ce,"Kamata ya yi a lura da kiki-kakar ciniki dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, lura da cewa tsarin cinikayyar kasashen biyu sun yi kama da juna sosai, kamar sana'ar sarrafa tufafi da dai sauransu. Game da wasu kasashen Afrika, kamar Afrika ta kudu kuwa, sana'ar dinkin tufafi da fitar da su zuwa kasashen waje ta zama wata muhimmiyar sana'a a kasar, kuma idan kasar Sin ta shiga sana'ar dinki tufafi ta Afrika ta kudu, hakan na iya kawo barazana ga wannan sana'a a kasar, sabo da haka, ba za a rasa kiki-kakar ciniki tsakanin bangarorin biyu ba. Ban da wannan kuma, yayin da wasu kananan kamfanoni na kasar Sin ke shiga kasar, sun yi amfani da tsarin tattalin arziki da dokar da ba ta da karfi, don yin ciniki ba bisa ka'ida ba, abin da ya kawo illa sosai ga kamfanonin wurin.

Game da raya makomar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, Qu Xing ya bayyana cewa, kasashen Afrika sun dau wani matsayi da ba za a canja ba a cikin manufar diplomasiyyar kasar Sin, kuma tabbas ne dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika za ta samu makoma mai haske.

Don gane harkokin cinikayyar bangarorin biyu, Qu Xing ya bayyana cewa, idan aka yi la'akari da inganta hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kamata ya yi masana'antu su yi la'akari da ba da gudummawa ga kasashen Afrika, wanda hakan zai yi amfani ga raya dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu, a sa'i daya kuma, a karkashin sabon yanayin da ake ciki, kulla dangantaka da jam'iyyun hamayya na kasashen Afrika shi ma yana da muhimmanci sosai, ya ce, "Inganta horar da kwararru da kulla kyakkyawar danganta da jama'ar kasashen Afrika, da karfafa ziyarar da ke tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Afrika na da muhimmanci sosai, a da, mun jaddada cewa, ba za a yi katsalandan game da harkoki cikin gida na kasashen Afrika ba, sabo da haka, ba za mu yi mu'amala mai zurfi da jam'iyyun hamayyar kasashen Afrika ba, a karkashin yanayin siyasa da ake ciki yanzu, akwai jam'iyyu daban daban a kasashen Afrika, sabo da haka, kamata ya yi mu kulla kyakkyawar dangantaka da jam'iyyu daban daban, don magance sauyin siyasa a kasashe.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China