in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara 14 sun rasu sakamakon wani hadarin mota da ya auku a tsakiyar Nijeriya
2013-08-05 13:14:51 cri
Kimanin yara 14 ne suka rasu, baya ga wasu 9 da suka jikkata, sakamakon wani hadarin mota da ya ritsa da su a karamar hukumar Barkin-Ladi da ke jihar Pilaton Nijeriya.

Rundunar 'yan sanda a jihar ce ta tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda ta ce, wata mota dauke da masara ce ta kwace, ta kuma yi kan wasu yara 'yan kimanin shekaru 12 zuwa 16, da ke motsa jiki da misali karfe 7 na safiyar Asabar 3 ga wata, lamarin da nan take ya haddasa rasuwar 14 daga cikin yaran.

Ya zuwa yanzu, wadanda suka samu raunuka na ci gaba da karbar magani a asibiti.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China