in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu karuwar wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin jihar Kano
2013-08-01 12:08:37 cri
Yawan mutane da suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai unguwar Sabon Garin Jihar Kano, dake Arewacin Najeriya ya karu zuwa mutum 45.

Jagoran al'ummar Igbo mazauna yankin na Sabon Gari Chief Tobias Idika ne ya tabbatar da hakan, yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin na Kano. Chief Idika ya kara da cewa, shi da ragowar jagororin yankin da wannan balahira ta auku, sun kirga gawawwakin mutane 45 da ke ajiye a wurin adana mamata, domin baiwa 'yan uwan wadanda harin na ranar Litinin ya ritsa da su damar bubawa.

Baya ga wadanda suka rasu sakamakon farmakin na ranar Litinin din data gabata, Chief Idika, ya kuma ce akwai karin wasu mutane 15 da suka samu raunuka, wadanda kuma a yanzu haka ke samun kulawar jami'an lafiya a asibitoci mallakar gwamnatin jihar daban daban. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China