Har ila yau rahotanni sun tabbatar da cewa za a rufe runfunan zaben ne da misalin karfe 6 na yammaci, a kuma sanar da sakamakon zaben nan da kwanaki 5 masu zuwa. Kimanin 'yan kasar ta Mali miliyan 6.8 ne ake sa ran za su sake kada kuri'unsu a wannan zagaye.
A wani labarin mai alaka da wannan kuma, jagoran tawagar jami'an sa ido ga zaben kasar ta Mali na kungiyar AU Edem Kodjo, ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar ta Mali da su fito kwansu-da-kwarkwata, domin kada kuri'unsu, Kodjo wanda ya yi wannan kira ranar Asabar 9 ga wata, ya ce zagayen zaben na farko ya gudana ba tare da wani korafin aikata magudi ba, don haka ya zama wajibi ga al'ummar kasar su baiwa zagayen na biyu cikakken muhimmanci da ya dace. (Saminu Alhassan)