A cewar wasu daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu da kuma isa tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, dake tsakanin Sicile da arewacin nahiyar Afrika, jirgin ruwan dake dauke da wadannan bakin haure ya nutse ruwa a ranar Jumma'a, kwanaki uku bayan ya fito daga gabar ruwan kasar Libiya. Jami'an tsaron iyakokin kasar Italiya sun samu ceto mutane 22 da suka fito daga kasashen Nijeriya, Gambiya, Benin da kuma Senegal.
A cewar kafofin kasar Italiya, kusan bakin haure 'yan Afrika 450 suka isa tsibirin Lampedusa a cikin kwanaki biyu na baya bayan nan, karamin tsibiri na fama da matsalar bakin haure dake neman samun zaman rayuwa mai kyau a kasashen Turai.
Dubun dubatar bakin haure suka mutu a yayin da suke kokarin shiga kasashen Turai daga arewacin Afrika da yankin kasashen larabawa. (Maman Ada)