Ranar Laraba 31 ga wata ne, aka yi wani gagarumin bukin cika shekaru 86 da kafa rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin wato PLA a ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Abuja na Najeriya. Jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Deng Boqing, babban jami'in dake kula da harkokin sojojin kasar Sin dake Najeriyar Kang Honglin, da sauran manyan jami'ai sun halarci bukin.
A cikin jawabin da ya gabatar, Mista Kang Honglin ya ce, sojojin kasar Sin da na sauran kasashen duniya, ciki har da na Najeriya, suna nan suna kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. Domin nuna goyon-baya ga aikin shimfida zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin yammacin Afirka, gwamnatin kasar Sin ta tura dakarunta zuwa kasashen Saliyo, Laberiya da kuma Cote d'Ivoire da zummar taimakawa wanzar da zaman lafiya. Haka kuma nan bada dadewa ba, kasar Sin zata tura sojoji dari hudu zuwa kasar Mali don gudanar da ayyukan shimfida zaman lafiya.
Kang Honglin ya kara da cewa, a cikin 'yan shekarun nan, rundunonin sojojin Sin da Najeriya suna yin hadin-gwiwa da yin mu'amala yadda ya kamata. Yayin ziyarar shugaba Goodluck Ebele Jonathan a kasar Sin kwanan nan, mukaddashiyar ministan tsaron Najeriya Dr. Elelu Olusola Obada tayi shawarwari tare da ministan tsaron kasar Sin Mista Chang Wanquan, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya daya kan karfafa hadin-gwiwa tsakanin sojojin kasashen biyu.
Mista Kang ya ce, hadin-gwiwar da ake yi tsakanin sojojin kasashen Sin da Najeriya, zai kara taimakawa Najeriya wajen inganta kwarewarta a fannin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin gida da waje.(Murtala)