in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Syria ya yi imanin kawar da ta'addanci
2013-08-19 10:27:41 cri

Shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad ya baiyana ranar Lahadi cewa, kasarsa za ta iya kawar da ta'addanci, yayin da dakarun gwamnati suka cimma nasarar sake kwato karin yankunan wajen garin Latakia dake bakin teku, inda kuma nan ne tsakiyar yanki da yake mulki.

Aassad ya baiyana hakan ne yayin wata ganawa da tawagar kasar Mauritaniya mai ziyara, inda shugaban dake fama da kalubaloli ya jadadda cewa, Syria tana maraba da dukkan wani kyakyawan yunkuri na warware rikici, kana a shirye take ta yi hadin gwiwar ayyukan kawar da ta'addanci da kasar ta shafe watanni 29 tana fama da shi.

Shugaban yana ganin yiwuwar hakan ne bayan da sojojin suka sake kwato Latakia, wanda ake dauka a matsayin cibiyar shugabancin gwamnatin Assad, in ji rahotannin daga kafofin labarai.

Kamfanin dillancin labarai mallakar kasar, SANA, ya baiyana cewa, sojojin sun kwato wasu kauyuka dake yankin arewacin Latakia.

Wannan nasara ta yiwu ne kwana daya bayan da sojojin suka kwato muhimman kauyukan na Latakia guda 3.

A makon da ya gabata, 'yan tawayen sun kai hari na kan mai uwa da wabi a kauyukan Latakia, a yunkurinsu na yin illa ga matsayin Assad a yankunan da yake mulki, inda kuma mafi yawan mutanen 'yan Alawite ne, wato wadanda suke da tushe da Shi'a, wanda kuma masu mulkin Syria suke ciki. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China