in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan gudun hijirar Syria da suka shiga Lebanon sun haura dubu 688, in ji wani rahoto na MDD
2013-08-19 15:44:38 cri

A ranar 18 ga wata, hukumar MDD mai kula da harkokin 'yan gudun hijira ta fidda wani rahoto a birnin Beirut, wanda ke cewa, ya zuwa yanzu, yawan 'yan gudun hijira da suka shiga kasar Lebanon daga kasar Sham ya haura dubu 688, adadin ya karu da dubu 11, idan aka kwatanta da na makon da ya gabata.

Rahoton ya kuma nuna cewa, mutane dubu 577 cikin wannan adadi sun riga sun yi rajista da hukuma mai kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD, yayin da saura dubu 110 ke jiran rajista da hukumar a nan gaba. A halin yanzu dai, gwamnatin kasar Lebanon, da MDD, da sauran hukumomin da abin ya shafa na ci gaba da lura tare da ba da taimako ga 'yan gudun hijirar.

Rahoton ya kuma kara da cewa, hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD, da hadin gwiwar mahukuntan dake lura da kan iyakar kasar Lebanon, na karfafa bincike kan takardun shaidar da 'yan gudun hijirar ta Sham ke dauke da su. Rahoton ya ce, 'yan gudun hijirar dake dauke da cikakkun takardun shaida ne kadai za su iya shiga kasar ta Lebanon, su kuma samu kayayyakin agaji da ake samar musu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China