in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadanda suka mutu a arangama da jami'an tsaro a Misra sun haura 525
2013-08-15 20:30:56 cri
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta fitar da adadin dake hannunta wanda ke nuna cewa a kalla mutane 525 ne ake da tabbacin sun rasa rayukansu, wadansu 3717 kuma suka ji rauni a sassa daban daban na kasar Masar.

Hakan kuwa ya biyo arangama da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsy suka yi da kuma jami'an tsaro, sakamakon cika wa'adin da gwamnati ta bayar cewa duk masu zanga zanga dake bisa tituna su waste daga manyan sansanoni biyu da masu zanga zanga suka yi gangami a Alkahira da kuma Giza. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China