in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji sun tare hanyar da ta ratsa cikin jihohin arewacin kasar domin zakulo 'yan ta'adda
2013-05-18 16:50:06 cri
A ranar Jumma'a 17 ga wata, mazauna garin Maiduguri suka bayyana cewa rundunar tsaro ta musamman da aka tura jihohin Yobe da ita kanta Borno da kuma Adamawa dake fuskantar tashin hankali kuma aka sanya ma dokar ta baci sunyi ma kan iyakokin da ya hada jihohin kewayanta domin hana 'yan ta'adda tserewa zuwa wassu jihohin dake makwabtaka dasu.

Wakilin kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua ya ce wannan kawanya an yi shi ne domin tabbatar da cewar wadannan 'yan ta'adda basu tsere ba ganin ana ta ma sansaninsu barin wuta.

A wani labarin kuma wadannan dakarun tsaron na musamman sun samu nasara wargaza wassu sansani a cikin dokar daji da 'yan ta'addan suka yi a arewaci da kuma tsakiyar garin na jihar Borno, kamar yadda Kakakin rundunar Tsaron kasar Chris Olukolade ya yi bayani ma manema labarai a garin Abuja a jiya Jumma'a, inda yace an tarwatsa manyan makamai da suka hada dana harbo jiragen sama da kuma bindigogin tankunan yaki duk a cikin wannan hari.

Olukolade yace wannan aiki na musammam da ya kunshi kara yawan jami'an tsaro yasa an cimma nasarar lalata kayayyakin 'yan ta'addan da yawa da suka hada da motocinsu da kuma inda suke adana man da suke amfani dasu har ma da injin din bada wutar lantarki.

A cewarsa za'a iya tantance yawan mutanen da aka kashe a bangaren 'yan ta'addan bayan kammala samamen a inda suke kuma hedkwatar rundunar sojan kasar dake Abuja ta gamsu matuka da wannan sakamako da aka samu da kuma kwazon da jami'an tsaron da aka tura suke nunawa yana mai basu kwarin gwiwwa dasu kara himma.

Yanzu haka dukkannin kan iyakokin jihohin uku an killace su sakamakon umurnin da Shugaban Najeriya ya bayar ga Babban Hafsan Tsaron kasar Ola Ibrahim kan aika da karin dakarun soji domin maido da tsaro a wadannan jihohin da 'yan ta'adda suke yadda suka so.

A ranar Talatar data gabata ne dai Shugaba Goodluck Jonathan ya sanar da kafa dokar ta baci a jihohin Adamawa,Yobe da Kuma Borno ganin yadda mazauna wurin ke fuskantar tashin hankali da barazana da ya kawo asarar rayuka da dukiyoyi daga wajen 'yan ta'adda.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China