in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka na aiki tukuru domin habaka ci gabansu, in ji wani kwararren Najeriya
2013-03-25 11:06:04 cri

Wani kwararre a harkokin da suka shafi huldodin kasa da kasa, kuma babban darakta a cibiyar nazarin harkokin kasashen waje a Nigeria Bola Akinterinwa, ya bayyana irin kyawawan matakai na hadin gwiwa dake wanzuwa tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afirka a 'yan shekarun nan, don gane da bunkasar ci gabansu.

Yayin wata ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, Akinterinwa ya bayyana cewa, irin gudummawar da kasar Sin ke baiwa kasashen nahiyar ta Afirka, na karfafa dangantakar dake tsakaninsu, tare da bunkasa ci gaban bangarorin biyu. A cewarsa, irin goyon bayan da Sin ke baiwa kasashe masu tasowa musmman ma Nigeira, ya sanya ta kasancewa babbar kawa a fannin dangantakar kasashen ketare. Akinterinwa ya kara da cewa, dandalin nan na hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, na taimakawa fahimtar juna tsakanin al'ummun kasar ta Sin, da kuma takwarorinsu na kasashen dake nahiyar ta Afirka.

Daga nan sai jami'in ya shawarci gwamnatin kasar ta Sin, da ta sanya karin kulawa ga batun musayar fasaha da nahiyar ta Afirka, tare da yada al'adunta a nahiyar, ta yadda al'ummar Afirka za su dada fahimtar kasar ta Sin dake nahiyar Asiya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China