Ofishin jakadancin Sin da ke kasar Tanzania da jami'ar Dar es salaam su ne suka hada kai wajen gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu, tare da aniyar karfafa musayar ilmi tsakanin Sin da Afirka, da kuma tattaunawa tare kan "burin Sin" da " burin Afirka" da kuma ci gaban dangantaka a tsakanin bangarorin biyu.
Masana kimanin guda ashirin wadanda suka zo daga kasashen Sin, Tanzania, Nijeriya, Kenya, Afirka ta Kudu da kuma Morocco sun tattauna tare a yayin taron kan yadda za a fuskanci dama da kalubalen da za a gamu da su cikin ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka, yadda za a iya cimma burin Sin da na Afirka gaba daya yayin da ake samun ci gaban dangantaka tsakanin bangarorin biyu, yadda za a inganta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, gami da yadda za a kyautata dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka don moriyar juna. (Maryam)