in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bama-bamai cikin motoci sun kashe mutane 21 da raunata 73 a Bagadazan Iraki
2013-08-16 11:51:34 cri

An samu fashewar bama-bamai cikin motoci ranar Alhamis a birnin Bagadaza na kasar Iraki, inda mutane 21 suka mutu, kana 73 suka samu rauni a yanayin hare-hare da aka shafe wata guda ana kaiwa wanda kuma ke nuna karuwar tashin hankali a kasar.

An yi hare-haren ne da tashin bom a motoci guda shida da kuma wani bom da ya fashe a gefen hanya a wurare guda shida masu cunkoson jama'a a birnin Bagadaza.

Daya daga cikin bom din motocin ya tashi ne a gundunar Alawi, kusa da unguwar da ofisoshin gwamnatin kasar suke, da ma wasu gine-ginen ofisoshin jakadanci na kasashen waje, inda mutane 4 suka mutu, kana 12 suka samu rauni, in ji wata kafa ta 'yan sanda da bata so kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua ta baiyana sunanta ba.

Wani bom din a mota shi ma ya fashe a wajen ajiyar motoci a gundumar Kadhmiyah dake arewacin Bagadaza, inda mutane 7 suka mutu, guda 20 suka ji rauni, in ji kafar.

Bugu da kari, an fuskanci fashewar bom na mota a unguwar Bad Al-Mu'dham a cikin birnin, inda a nan ma mutane 5 suka mutu, 13 kuma suka samu rauni.

Hakazalika, wasu bama-bamai sun tashi cikin motoci guda biyu a lokaci guda a titin al-Qanat a gabashin birnin, kuma a nan ma mutane 2 sun mutu, guda 10 kuma suka yi rauni.

Wani bom na mota ya fashe shi ma a Shurta al-khamsa dake kudu maso yammacin Bagadaza tare da hallaka mutane 3, kana 11 suka yi rauni.

A unguwar Amil, bom ya tashi a can din ma a wata hanya, to amma mutane 7 sun yi rauni. Zuwa yanzu dai babu kungiya da ta dau alhakin wadannan hare-hare, to amma mafi yawan lokaci, kungiyar Al-Qaida a Iraki ita ce take kai wadannan hari na kunar bakin wake a kasar.

An yi wadanan hare-hare ne duk da cewar, praminsitan kasar Nuri Al-Maliki ya sha alwashi ranar Laraba da ta wuce cewa, za'a ci gaba da yaki da kungiyoyi masu tada kayar baya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China