A ranar Laraba, babban jami'in MDD a kasar Iraki ya yi suka da kakkausar murya dangane da munanan hare-hare da suka yi sanadin salwantar rayukan jama'a da dama a fadin kasar.
Wakilin magatakardan MDD na musamman kuma shugaban shirin ba da tallafi ga kasar Iraki (UNAMI) Martin Kobler ya ce, 'yan ta'adda sun sake kai muggan hare-hare kan jama'a bayin Allah dake fafutukar gina rayuwarsu don samun kyakyawan makoma wa kansu da 'ya'yansu, in ji mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey.
Mutane akalla 35 sun rasa rayukansu, kana 151 sun samu rauni ranar Talata, a hare-haren da aka kai a fadin kasar Iraki, mafi yawa a babban birnin kasar Bagadaza.
Del Buey ya bayyana wa manema labarai yayin ganawa ta yau da kullum cewa, wajibi ne a daina irin hakan, in ji Kobler.
Hakazalika, wakilin na musamman ya bukaci mahukuntan kasar Iraki da su yi iyakacin kokarinsu da kuma daukar matakan kare farar hula daga zub da jini, in ji del Buey. (Lami)