Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kasar Sin tana kira ga dukkan bangarori da ke kasar Masar, da su kwantar da hankali tare da warware dukkan bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari.
Mr. Hong Lei ya ce, kasar Sin tana mai da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Masar, kuma ta damu matuka game da halin da kasar ke ciki, ya kuma bayyana hakan ne lokacin da ya ke bayani game da matakin da 'yan sandan kasar Masar suka dauka na kawar da sansanonin masu bore a Alkahira, inda magoya bayan hambararren shugaba Mohamed Morsi suka hallara.
A cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Masar, mutane 278 ne suka mutu, ciki har da 'yan sanda 43, yayin da sama da mutane 2,000 suka jikkata a sassan kasar sakamakon matakin da jami'an tsaro suka dauka na tarwatsa masu boren.
Mr. Hong Lei ya ce, kasar Sin tana fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa, za su bayar da muhimmanmci ga muradun kasar da kuma al'ummar kasar, kana su yi hakuri tare da kaucewa karin jikkata.
Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari tare da maido da doka da zaman lafiya a kasar. (Ibrahim)