in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta kara tsawon lokacin tsare hambararren shugaba Morsi
2013-08-13 10:42:27 cri

kasar Masar ta kara tsawon lokacin da za ta cigaba da tsaren hambararren shugaba Mohammed Morsy da kwanaki 15 nan gaba bisa zargin hada baki da kungiyar Hamas, in ji kafar yada labaran ta yanar gizon kasar Al-Ahram ta bayyana.

A cikin bayanin, an ce, alkalin da ma'aikatar shari'ar da kasar ta nada domin yin binciken ya ba da umurnin a kara tsawon kwanakin 15 na cigaba da tsare Morsy domin a samu cikakken lokacin da za'a gudanar da bincike game da liken asiri ma kungiyar Hamas, reshen kungiyar 'yan uwa Musulmi na kasar Falasdinu, jam'iyyar da ta tsai da Morsy takara tun da farko.

Sai dai kuma alkalin Hassan Samir wanda da farko shi ya fara dora takunkumi a kan shari'ar bai sanar da wannan shawara a hukumance ba, kamar yadda Al-Ahram ta jiyo labarin hakan daga wata majiyar ma'aikatan shari'ar ana da shi a ran nan da wassu 'yan kwanaki masu zuwa.

Ana dai zargi Morsi ne da hada alaka da kungiyar Hamas a lokacin zanga-zangar da aka yi a watan Janairun shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyar sauke tsohon shugaba Mubarak daga mulki, sannan kuma ya yi amfani da wannan zanga-zanga, aka yi barna a harabar hukumar 'yan sanda da cin zarafin jami'an 'yan sandan, sakin fursunoni daga gidan kaso, tare kuma da cinna wuta a gidan yarin Wadi al-Natron, inda aka taba tsare shi a da can. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China