in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi suka dangane da tashin hankali a Masar
2013-08-15 10:50:56 cri

A ranar Laraba, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya yi suka kan tashin hankali da zubar da jini na baya bayan nan a kasar Masar, inda ya kira lamarin 'babban koma baya ga yunkurin sulhu a kasar'.

Babban jakadan na kasar Amurka yayin da yake karanta wani rubutaccen jawabi da aka saba bayarwa kullum ya ce, wannan abu babban koma baya ne ga sulhu a Masar da kuma burin jama'a na samun sauyin demokradiya da shiga cikin harkokin kasar.

Ya kara da cewa, al'amuran da suka auku a wannan rana abin kyama ne kuma sun saba da burin jama'ar Masar na samun zaman lafiya, shiga harkar shugabanci da samun demokradiya ta asali.

Kafofin talbijin na kasar sun ba da rahotanni mutuwar akalla 'yan sanda 43, kana 211 sun samu rauni yayin arangama da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi, lokacin da 'yan sandan ke kokarin korar masu zanga-zanga a babban birnin kasar, Alkahira.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Masar ta baiyana cewa, yunkurin 'yan sanda na kawar da jama'a daga sansanin ya yi sanadin arangama a fadin kasar, inda mutane 149 suka mutu, kana 1400 suka samu rauni.

Sakataren harkokin wajen na Amurka Kerry, ya kara da cewa, ya kamata 'yan kasar Masar dake ciki da wajen gwamnati su sake yin nazari, su kuma kwantar da hankali don a kauracema karin asarar rayuka. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China