in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabbin gwamnoni a Masar
2013-08-14 09:40:26 cri

Gwamnatin riko ta kasar Masar ta rantsar da gwamnoni wa daukacin gundumomin kasar illa guda biyu, in ji rahoton da kamfanin dillancin labaran kasar, MENA, ya bayar ranar Talata.

Garambawul din da aka yi ya kunshi gwamnoni guda 18, guda shida za su ci gaba kan matsayinsu, kana an yi wa guda daya sauyi daga gundumar Red Sea zuwa Alexandria.

To amma kuma, ba'a nada sabbin gwamnoni wa Red Sea da Minufiya ba.

Baki daya dai akwai gundumomi guda 27 a kasar Masar. Galal al-Saeed shi ne aka nada a matsayin sabon gwamnan babban birnin kasar, Alkahira. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China