in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar al'ummar Falesdinu ya gana da ministan harkokin wajen Amurka
2013-04-08 14:08:28 cri
Bayan ziyararsa a kasar Turkiya, ran 7 ga watan Afrilu, ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya yi shawarwari tare da shugaban hukumar al'ummar Falesdinu Mahmoud Abbas a yammacin gabar kogin Jordan, inda suka yi tattaunawa kan harkokin farfado da shawarwarin zaman lafiya da ke tsakanin Falesdinu da Isra'ila da dai sauran wasu batutuwa.

Wannan ita ce ganawa ta uku tsakanin manyan jami'an biyu a cikin wata guda. Kuma kafin ganawarsu ta wannan karo, bisa labarin da aka samu daga bangaren Falesdinu, an ce, kasar Amurka ta shirya wannan ganawa, saboda kasar Falesdinu ta riga ta bayyana matsayinta kan batun a lokacin ziyarar shugaba Barack Obama na kasar Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya a karshen watan Maris, shi ya sa Mahmoud Abbas ya gana da John Kerry a wannan karo, domin sanin ko akwai wasu sabbin shawarwari, ko a'a. Ya zuwa yanzu, Falesdinu da Isra'ila ba su gano hakikanin shiri ko sabbin dabarun da kasar Amurka ta gabatar kan batun farfado da shawarwarin zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China