Kasar Ghana ta bayyana niyyarta na kafa wani sabon kamfanin jiragen sama na kasa a daidai lokacin da wannan bangare na sufuri yake bunkasa a wani labari da ya fito daga bakin ministar sufurin kasar Ghana, madam Dzifa Aku Ativor a ranar Talata. 'Muna son tarmamuwa baka ta kasarmu, dake matsayin tambari na tsohon kamfanin jiragen sama na Ghana Airways ta dawo a cikin sararin samaniya domin jin dadin al'ummar kasar Ghana baki daya.' in ji minista Dzifa Aku Ativor a yayin da take hira tare da 'yan jarida.
Kamfanin jiragen sama na Ghana Airways (GA) ya kasa tada kai, dalilin haka ne aka rushe shi a shekarar 2005.
Kamfanin jiragen saman kasa da kasa na Ghana Airlines (GIA), an kafa shi ne domin ya maye gurbin tsohon a matsayin wata sabuwar dama, haka kuma kamafanin Ghana Airways ya mutu dalilin rashin biyan bukatunsa na kudi.
Yawan fasinjoji cikin gida da na waje dake daukar jiragen sama na dadada karuwa ko da yaushe daga kashi 15 cikin 100 a shekarar 2010, kashi 17 cikin 100 a shekarar 2011 da kuma kashi 27 cikin 100 a shekarar 2012.
Bisa tsarin fadada harkokin sufurin jiragen sama na kasar Ghana ne za'a gina sabon filin jirgin sama a Prampram, kusa da Tema mai tazarar kilomita 30 daga gabashin birnin Accra, domin zirga-zirgar jiragen saman kasa da kasa dake zuwa Ghana a yayin da su kuma filayen jiragen sama na yanzu ake cigaba da gyare-gyarensu da fadada su, ta yadda za su iyar karbar yawan fasinjojin dake cigaba da karuwa, in ji madam Ativor. (Maman Ada)