A ranar Alhamis da dare ne shugaba John Dramani Mahana na kasar Ghana, ya tashi zuwa kasar Equatorial Guinea don halartar taron kolin kasashen da ke yankin tekun Guinea da za a yi a birnin Malabo, babban birnin kasar.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta Ghana ta bayyana cewa, shugaban Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ne zai shugabanci taron, wanda zai mayar da hankali kan tsaron jiragen ruwa a yankin tekun Guinea.
Ana sa ran shugaba Mahama wanda ya sha magana game da karfafa matakan tsaron jiragen ruwa a kan iyakokin kasashe da takwarorinsa da ke kasashen Cote d'Ivoire, Togo, Benin da kuma Najeriya, zai gabatar da muhimman shawarwari a wajen taron kolin.
Kasar ta Ghana dai ta kara inganta na'urorin da sojojin ruwanta ke amfani da su a shekaru ukun da suka gabata, kuma a baya-bayan nan ta kafa sashen 'yan sandan kula da jiragen ruwa da nufin sa-ido kan masu fashin jiragen ruwa da kare na'urorin mai da iyakokin ruwan kasashen da ke yammacin Afirka.
Fadar shugaban kasar ta Ghana ta ce, a ranar Asabar ne ake sa ran shugaba Mahama zai dawo gida. (Ibrahim)