Hukumar lura da harkokin ma'adanai a kasar Ghana, ta ce, an sake gano wasu karin wuraren hakar nau'o'in ma'adanin karfe da dama a yankin Nkwanta dake arewacin Volta, ana kuma ci gaba da bincike kan wadannan ma'adanai domin tantance yawansu.
Babban jami'in hukumar Benjamin Aryee ne ya bayyana hakan ranar Laraba 10 ga watan nan na Yuli, yayin jawabinsa a wurin bikin bude taron yini biyu, na masu ruwa da tsaki kan batun bunkasa harkokin zuba jari da samar da ci gaba, a fannin hakar ma'adanai na kasahen nahiyar Afirka na bana mai lakabin AMIDS. Aryee ya kara da cewa, an gano wadannan wurare ne tun a shekarar 2010, karkashin shirin tallafawa sashen hakar ma'adanai da kungiyar tarayyar Turai ke baiwa agaji.
Da yake karin haske don gane da alfanun wannan ci gaba ga kasar ta Ghana, Aryee ya ce, hakan zai ba da damar fadada arzikin kasar ta fuskar ma'adanai, ya kuma rage karfin farashin da zinari ke da shi a sashen ma'adanai da ma tattalin arzikin kasar baki daya. Har ila yau, jami'in ya bayyana wa mahalarta taron cewa, kasar ta Ghana za ta ci gajiya mai yawa daga wannan sashe, da zarar an fara aikin hakar ma'adanan daga wadannan wurare. (Saminu)