A cikin wannan shirin doka, an kayyade fannonin da 'yan kasuwan kasashen waje za su zuba jari da kuma hanyoyin da za su bi da dai sauransu.
Har wa yau, shirin dokar ta kara yawan kudin yin rajista mafi kankanta wanda tilas ne 'yan kasuwan kasashen waje su biya, wato wadanda suka shirya zuba jari a cinikayyar sari, daga dalar Amurka dubu 300 zuwa dalar Amurka miliyan 1. Sa'an nan ta bukaci dukkan masana'antu, ciki had da na wurin, su yi rajista a cibiyar bunkasa harkokin zuba jari ta kasar.
Gwamnatin Ghana ta nuna cewa, za ta ci gaba da sa kaimi ga 'yan kasuwan kasashen waje da su zuba jari a harkar cinikayya da dai makamantansu, su kuma kyautata darajar kayayyakinsu, da samar da guraben aikin yi ga mazauna wurin, kana da karfafa karfinsu na raya kansu a kasar ta Ghana.(Tasallah)