in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun kolin Ghana ta tsai da ranar yanke hukunci game da zaben kasar
2013-08-08 14:09:38 cri

Kotun kolin kasar Ghana ta tsai da ranar Laraba 29 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta yanke hukunci game da karar da aka shigar na kalubalantar zaben shugaba John Dramani Mahama a matsayin shugaban kasar ta Ghana da ke yammacin Afirka.

Kotun ta bayar da wannan sanarwa ce bayan sauraron shaidun baka da jam'iyyun da suka shigar da karar suka bayar a ranar Laraba da safe.

Shugaban tawagar alkalan da ke sauraron karar, mai shari'a William Atuguba, ya ce, kotun za ta zauna a ranar Laraba mai zuwa don tantance sahihancin shaidun da dukkan bangarorin suka gabatar ta yanke hukunci bayan kwanaki 15.

Hukumar zaben kasar Ghana ce ta ayyana shugaba Mahama a matsayin wanda aka zaba, kwanaki biyu bayan babban zaben kasar da ya gudana a ranar 7 ga watan Disambar shekara ta 2012.

A cewar hukumar zaben, Mahama ya samu kashi 50.7 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da abokin takararsa Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na jam'iyyar NPP ya samu kashi 47.7 cikin 100. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China