Bisa aniyarta ta rungumar shirin wanzar da zaman lafiya tsakaninta da al'ummar Falasdinu, Isra'ila ta saki firsinoni Falasdinawa 26 da take tsare da su, inda rahotannin baya bayan nan ke cewa, tun da sanyin safiyar Larabar nan, mutanen da aka saka suka isa yankunansu dake yammacin gabar kogin Jordan da kuma zirin Gaza.
Wadanda suka shaida sakin firsinonin sun ce, 11 daga cikinsu, an dauke su a wata babbar mota zuwa Bitunia, dake kusa da birnin Ramallah, a hanyarsu ta shiga yankin yammacin gabar kogin Jordan, yayin da kuma aka kai ragowar 15 dake kan hanyarsu ta shiga zirin Gaza zuwa Erez, dake kan iyakar Falasdinu da Isra'ila.
Iyalai da 'yan uwan wadanda aka saki sunyi dafifi a kusa da wuraren biyu, rike da tutocin Falasdinu, da alluna masu dauke da sakwanni daban daban suna dakon zuwan 'yan uwan nasu. (Saminu)