in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yahudawa da Palasdinawa sun tsai da ranar sake tattaunawa a birnin Kudus
2013-08-09 10:30:10 cri

Ma'aikatar kula da harkokin kasashen wajen Amurka ta fada a ranar Alhamis cewa, a ranar 14 ga watan Agusta ne bangaren Isra'ila da Palasdinu za su gudanar da zagaye na biyu na tattaunawarsu a birnin Kudus.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Jen Psaki ce ta bayyana hakan ga manema labarai, inda ta ce, bayan ganawa tsakanin bangarorin biyu, za kuma a yi wata ganawar a garin Jericho.

Ta kuma bayyana cewa, manzon Amurka kan kokarin wanzar da zaman lafiya Martin Indyk da mataimakinsa Frank Lowenstein za su tashi zuwa shiyyar, don ganin tattaunawar ta gudana yadda ta kamata, sai dai sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ba zai bayar da wata sanarwa ba bayan taron.

Isra'ila da Palasdinawa sun amince su kara ganawa ne domin su tattauna dukkan matsayin batutuwan da ke tsakaninsu, kamar matsayin birnin Kudus, tsaro, matsugunan Yahudawa, batun kan iyaka da 'yan gudun hijira da sauransu, bayan da manyan masu shiga tsakaninsu suka gana a karshen watan da ya gabata a birnin Washington don fara tattaunawar da aka shirya ta kwanaki biyu.

Bugu da kari, Psaki ta ce, Kerry da mai baiwa shugaba Obama shawara kan harkokin tsaro Susan Rice, za su yi wata tattaunawa ta daban da Amurkawa Yahudawa da kuma shugabannin al'ummar Amurkawa Larabawa a ranakun Alhamis da kuma Jumma'a da yamma a fadar White House.

Psaki ta ce, wadannan ganawa za su samar da wata damar yiwa shugabannin al'ummomin karin haske game da alkibla ta karshe kan sake maido da tattaunawa tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, da kuma jin ta bakin shugabannin wadannan al'ummomi kai tsaye game da ra'ayinsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China