Shugaban al'ummar Palesdinu Mahmoud Abbas a jiya Lahadi ya nada wani malamin makaranta mai zaman kanshi Rami Al-Hamadallah domin ya jagoranci sabuwar gwamnatin, inda zai maye gurbin tsohon firaminista Salam Fayyad.
Abbas ya kira Al-Hamadallah zuwa ofishinsa, inda ya mika masa wannan bukatar tasa, wassu majiyoyi sun nuna cewa, shi dai Hamadallah wanda shaihun malami ne a fannin harsuna a jami'ar Al-Najah, tuni har ya amince da wannan bukata.
Majiyoyi sun nuna cewa, Al-Hamadallah zai fara aikin nada ministocinsa nan take a cikin makonni uku masu zuwa kamar yadda dokar Palesdinu ta tanadar. Sai dai kuma kafa sabuwar gwamnati ba ta da wata alaka da sulhun da aka yi tsakanin jam'iyyar Abbas ta Fatah da kuma jam'iyyar adawa ta Hamas da aka yi a shekarar 2011, wanda a cikin yarjejeniyar sulhu, Abbas zai jagoranci gwamnatin hadin gwiwwa har lokacin babban zabe. Sakamakon amincewa da ajiye aikin da Salam Fayad, babban masanin tattalin arziki da kasar Amurka ke mara ma baya, Abbas ya yi alkawarin sake nada gwamnatin da za ta yi aiki da bangaren Hamas, wadanda suka amshe Gaza daga magoya bayan Abbas a 2007, sai dai har yanzu bangarorin biyu ba su amince da wassu muhimman batutuwa a tsakanin su ba.(Fatimah)