Rahotanni daga kasar Kenya na nuna cewa, an fara gudanar da kwarya-kwaryar aikace-aikace, na sauka da tashin jiragen sama a filin Jomo Kenyatta da maraicen ranar Laraba, bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen da aka yi, sakamakon tashin wata gobara da sanyin safiyar wannan rana, lamarin da ya haddasa lalacewar wasu sassan ginin filin jirgin.
Babban sakatare a ma'aikatar sifiri da bunkasa ababen more rayuwa injiniya Michael Kamau ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai. Kamau ya ce, ma'aikatan dake aikin gyaran sassan filin jirgin na ci gaba da kokari ba dare ba rana, don ganin an kammala gyaran sashe na 2 da na 3, na zauren sauka, da tashin fasinjojin dake zirga-zirga tsakanin manyan kasashen duniya ta wannan filin jirgi.
A nasa bangare, babban shugaban hukumar gudanarwar filin jirgin na Jomo Kenyatta, Mr. Titus Naikuni, ya ce, kawo yanzu ba a kai ga fara cikakken aiki a filin jirgin ba.
Da sanyin safiyar ranar Labara ne dai wata gobara, da kawo yanzu ba a tantance musabbabin tashin ta ba, ta lankwame wani sashe na filin jirgin, kafin daga bisani masu aikin ceto su shawo kanta. Mahukuntan kasar ta Kenya sun tabbatar da cewa, ba a samu hasarar rayuka sakamakon aukuwar gobarar ba. (Saminu)