Gwamnatin kasar Kenya ta ba da bayani ranar Alhamis cewa, babban filin jirgin sama na kasar zai fara sufurin kasa da kasa daga daren wannan rana bayan da wata gobara ta kona sashen isowar fasinjoji a filin jirgin saman, da aka saba kaiwa da komowa.
Ministan sufuri da bunkasa ababan jin dadin rayuwa Michael Kamau ya baiyanawa 'yan jarida a birnin Nairobi cewa, jami'an tabbatar da tsaro na hukumar filayen jiragen sama na kasar Kenya (KAA), za su ci gaba da ba da bayanai na tsaro ga sauran ma'aikata don a tabbatar da kasancewar lafiya da cikakken tsaro ga jama'a.
Kamau wanda ke bayani yayin wata ganawa da 'yan jarida ya ci gaba da cewa, hukumar sufurin jiragen sama ta kasar Kenya (KCAA), ta tabbatar ta hanyar shawarwari cewa, ana iya maido da sufurin kasa da kasa daga daren Alhamis a filin jiragen sama na JKIA.
Kamau ya ba da wannan bayani ne bayan da aka fara maido da sufurin kasa da kasa a filin jiragen sama na Jomo Kenyatta sakamakon tashin gobara, wacce ta yi sanadin rufe wannan muhimmin filin jiragen saman.
KAA ta bada tabbaci ranar alhamis da safe cewa wasu jiragen sama na kasa da kasa sun maido da harkokinsu a filin.
Jiragen Kenyan Airways guda biyu da suka taso daga kasar Turai da gabashin duniya sun sauka a filin jiragen ranar Alhamis da safe yayin da jami'an gwamnati ke kokarin tabbatar da gudanarwar harkoki yadda aka saba. (Lami)